WAYE BLOGGER
BLOGGER Blogger shi ne mutumin da yake rubuce-rubuce a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi rayuwa a shafukan yanar gizo. Za ka iya zama cikekken ‘blogger’ idan ka mallaki website, ko blogsite a Google Blogspot da WordPress da sauransu, ta manhajojinsu ko kuma shafukansu AMFANIN BLOG Neman kudi Idan ka buɗe shafi a Google Blogspot.com kana iya samun kamar 300 visitors a kowacce rana, yawan samun waɗannan traffic zai baka damar ɗora tallace-tallace (ads) za su (iya) biyan ka miliyoyin kuɗaɗe a duk watan duniya. Wallafa (Publishing) A matsayin FREELANCER, za ka iya amfani da blogsite, domin wallafa rubutunka, ba tare da kana biyan so sisi ba. Tallace-tallace Ana iya tallata kaya ta blogsites kyauta, kamar a website. MATAKIN BUƊE BLOG PLATFORM(S) • GOOGLE BLOGPOT Ka mallaki email Idan da Blogspot za ka yi amfani wajen buɗe blogsite, da GMAIL kaɗai ake amfani. Ka buɗe ‘app’ (Blogger) ko shafin blogspot.com. Sai ka sa GMAIL naka wajen SIGN-IN. A shafin farko na Blogspot, za ka ga CREAT...