WAYE ELON MUSK
Elon Musk.
Darajar kamfanin Tesla da ke ƙera motocin lataroni na Elon Musk ta ƙaru a 2021, kuma darajarsa a kasuwa ta kai dala biliyan 700.
Hakan ya sa kamfanin na motoci ya zarta Toyota da Volkswagen da Hyundai da GM da kuma Ford idan an hada su baki daya.
Arzikin ɗan kasuwar mai shekara 51 ya ƙaru daga dala biliyan 127.9 zuwa dala biliyan 185 sakamakon haɓakar hannun jarin kamfanin Tesla, kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito.
A shekarar 2020 kaɗai, dukiyar Musk ta ƙaru da dala biliyan 100.3, kuma babu wanda ya samu ƙaruwar dukiya kamar wannan a jerin masu kuɗin duniya guda 500 na jaridar ta Bloomberg.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwitta ya kuma bar shi daga sama-sama, mai kuɗin ya ce: "Ina da niyyar amfani da rabin dukiyata wajen magance matsalolin da duniya ke fuskanta, sannan rabin kuma ina son samar da wani birni a duniyar Mars inda dukkan abubuwa masu rai za su iya ci gaba da rayuwa a can, ko da a ce wata rana duniyar Earth za ta ci karo da wani bala'i kamar na wasu manyan halittu irin su (dinosour) ko kuma Yaƙin Duniya Na III ta yadda za mu halaka kawunanmu."
Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani a game da shi:
Lokacin da yana yaro, likitoci sun nemi a duba lafiyar kunnensa saboda yawan tunani
An haifi Elon Musk ranar 28 ga watan Yunin 1971 a Pretoria na Afirka ta Kudu.
A shekarar 1988 Musk ya samu takardar zama ‘dan kasar Kanada, ya bar Afrika ta kudu, a wancan lokaci ne ya tattara ya koma Amurka.
Musk ya yi karatu ne a jami’ar Queen’s University ta Ontario. A 1992 ya koma jami’ar University of Pennsylvania a Philadelphia ya samu Digiri a ilmin tattalin arziki da kimiyya. A 1997 ya nemi ya fara digirgir a jami’ar Stanford University, amma sai ya watsar.
Tun yana yaro Musk yake yawaita tunane-tunane na ƙirƙirar abubuwa, abin da ta kai har sai da iyayensa da likitoci suka nemi a duba lafiyar kunnensa sakamakon rashin sauraron abubuwa.
Bayan mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, Musk ya fara sha'awar na'urar kwamfuta. Ya koya wa kansa yadda ake ƙirƙirar shafin intanet yana shekara 10. Ya sayar da manhajar da ya ƙirƙira ta farko yana shekara 12.
Ya kafa shafin X.com a 1999, wanda daga baya ya koma PayPal, sannan ya kafa SpaceX a 2002 da kuma Tesla Motors a 2003.
Tun yana shekara 20 ya zama miloniya bayan ya sayar da wani kamfaninsa mai suna Zip2.
Haɓakar dukiyar tasa ta faru ne akasari saboda kamfanin Tesla, wanda kimarsa ta kai kusan dala biliyan 500.
Kusan uku cikin huɗu na dukiyar sun samu ne sakamakon hannayen jarin Tesla, wanda darajarsa ta haɓaka fiye da sau huɗu idan aka kwatanta da na kamfaninsa na Space Exploration Technologies Corp - wanda aka fi sani da SpaceX.
Ya mayar da kansa rumbun ilimi
Elon Musk na tsananin ƙaunar karanta litattafai a rayuwarsa.
Lokacin da yake ɗan shekara tara da haihuwa, ya zama wani rumbun binciken ilimi kamar Encyclopaedia Britannica saboda yawaita bincike kan abubuwan da yake nema.
Hatta a yanzu, idan zai ɗauki ma'aikaci a kamfaninsa sai ya tabbatar ya san kaso mai yawa na ilimin mutum ta yadda ko da bai yi nasarar samun aikin ba, an ƙaru da iliminsa.
Ba ya son mallakar gida
A watan Mayun 2020 ne Musk ya ce ba zai sake mallakar wani matsuguni ba da sauran kayayyaki, inda ya saka gidajensa a kasuwa.
An yi wa gidajensa biyu da ya saka a kasuwa farashin dala miliyan 40 - ɗaya daga ciki ya saye shi ne daga hannun tauraruwar fina-finai Gene Wilder a 2013.
An yi wa gidan farashin dala miliyan tara da rabi, yayin da aka yi wa ɗayan farashin dala miliyan 30.
Aure
Attajirin ya hadu da mai dakinsa Justine Wilson a lokacin da suke karatu a jami’a. Daga baya sun rabu bayan Sun Gaifi ‘ya ‘ya biyar, A 2008 Musk ya hadu da Talulah Riley, bayan ‘yan shekaru suka yi aure. A 2012 masoyan suka rabu da juna, amma daga baya su ka sake aure. A 2014 sai aka ji Musk yana neman rabuwa da Riley, sai maganar ta mutu. A 2016 sakin ya tabbata, attajirin ya sake sakin sahibar ta sa.
A 2018 ne Musk ya auri wata Mawakiya mai suna Grimes wanda ta haifa masa wani yaro da aka sanyawa suna 'X Æ A-12.'
Yana bacci a kan kujerar ofis
Attajirin kan je aiki kamfaninsa kamar kowane ma'aikaci kuma har ma yakan kwana a can idan aiki ya yi masa yawa.
Yakan kwana a kan kujera saɓanin katifa ko gado, duk da cewa zai iya yin hakan idan yana buƙata.
Ya bayyana a wani littafinsa cewa yana iya sanin kaso mai yawa na ilimin mutum yayin da yake yi masa tambayoyin ɗaukar aiki a kamfaninsa ba don komai ba sai don gudun kar ma'aikacin ya gaza yin nasarar samun aikin.
@saliadeen cisey
Comments
Post a Comment