Muhammadu Buhari: 'Mu saka waɗanda rikicin ta'addanci ya rutsa da su cikin addu'a'

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci duka ƴan Najeriya su saka waɗanda rikicin ta'addanci ya rutsa da su cikin addu'a. Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wani jawabi da ya yi a ranar dimokraɗiyya ta ƙasar.

Shugaba Buhari ya ce kullum yana kwana yana tashi da baƙin cikin waɗanda aka yi garkuwa da su inda ya ce shi da duka hukumomin tsaron ƙasar na yin duk mai yiwuwa domin ceto waɗanda aka sace.

A yayin jawabin na shugaban ƙasar, ya soma ne da bayani kan muhimmancin ranar dimokraɗiyya inda ya jaddada muhimmancin zaɓen Yunin 1993 a tarihin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce kada ƴan Najeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokraɗiyya suka bayar a 1993. Ya buƙaci ƴan Najeriyar da su yi koyi da kishin ƙasa irin na magabata a duk lokacin da za su zaɓi shugabanni.

Comments

Popular posts from this blog

Four suspected cases of Monkeypox reported in Borno

Buhari gives Education Minister two weeks to settle ASUU strike............

CIKAKKEN TARIHIN BABBAN MALAMIN HADISIN NAN SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEN ALBANY