WAYE BLOGGER
BLOGGER
Blogger shi ne mutumin da yake rubuce-rubuce a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi rayuwa a shafukan yanar gizo. Za ka iya zama cikekken ‘blogger’ idan ka mallaki website, ko blogsite a Google Blogspot da WordPress da sauransu, ta manhajojinsu ko kuma shafukansu
AMFANIN BLOG
Neman kudi
Idan ka buɗe shafi a Google Blogspot.com kana iya samun kamar 300 visitors a kowacce rana, yawan samun waɗannan traffic zai baka damar ɗora tallace-tallace (ads) za su (iya) biyan ka miliyoyin kuɗaɗe a duk watan duniya.
Wallafa (Publishing)
A matsayin FREELANCER, za ka iya amfani da blogsite, domin wallafa rubutunka, ba tare da kana biyan so sisi ba.
Tallace-tallace
Ana iya tallata kaya ta blogsites kyauta, kamar a website.
MATAKIN BUƊE BLOG PLATFORM(S)
• GOOGLE BLOGPOT
Ka mallaki email
Idan da Blogspot za ka yi amfani wajen buɗe blogsite, da GMAIL kaɗai ake amfani.
Ka buɗe ‘app’ (Blogger) ko shafin blogspot.com.
Sai ka sa GMAIL naka wajen SIGN-IN.
A shafin farko na Blogspot, za ka ga CREAT YOUR BLOG, sai ka shiga.
sai ka saka PAGE TITLE (misali SAMPLE USER), sai ka yi NEXT.
Za ka zaɓi URL (sunan shafi), misali ‘usersampling.blogspot.com’ [idan akwai mai irin wannan URL din, za su ce ma, “SORRY, THIS BLOG ADDRESS IS UNAVAILABLE” ko “INVALID OR NOT SUPPORT” (idan ka yi amfani da wasu symbol, ko Kalmar da bata dace ba)], sai ka NEXT.
Shikenan, ka mallaki shafin blog da Google Blogspot.
• WORDSPRESS
Ka yi amfani da email.
Idan kuma da WordPress ne, za ka iya amfani da kowanne irin ‘email account’ (Gmail, Yahoo Mail, Hotmail…).
Ka buɗe ‘app’ (WordPress) ko shafin wordpress.com.
Idan ta website ne (wordpress.com), ka shiga GET STARTED ko START YOUR WEBSITE. Sai ka sa EMAIL, USERNAME da PASSWORD, za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.
Idan ta ‘app’ ne, za ka shiga LOGIN OR SIGN UP WITH WORDPRESS. Sai ka sa EMAIL, ka danna CONTINUE. za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.
Ka bu ɗe EMAIL, ka bu ɗe saƙon WORDPRESS ta inbox, sai ka pressing kan SIGN UP.
Idan a ‘app ne’ za zaɓi topic (misali, Food, Lifestyle, News, Personal, Photography…), ko kuma ka yi SKIP.
Za ka zaɓi THEME, sai ka CHOOSE.
Za ka zaɓi sunan DOMAI, misali, digitalusersample.wordpress.com.
Za su buɗe ma shafi YOUR SITE HAS BEEN CREATE, sai ka pressing OK
WALLAFA A BLOGSITE
Hanya mafi sauƙi ta yin publishing a BLOGSITES it ace, yin amfani ‘apps’ (Blogger/Wordpress) ko kuma ta computer (da browser).
Akwai sauran sites da za ka iya blogging da su kamar Wix.com, Medium.com, Weebly.com da sauransu.
✍️Aliyu M. Ahmad
17th Dhul-Hijjah, 1443AH
16th July, 2022CE
Comments
Post a Comment