FARKON KALANDAR MUSULUNCI WADDA MUSULMI SUKE AMFANI DA ITA
FARKON KALANDAR MUSULUNCI 622.
A Rana Mai Kamar Ta Yau 16 Ga Watan Yuli 622 A ka Kaddamar Da kalandar Musulunci Ta Farko.
Hijira ko hijirar Annabi a shekara ta 622 miladiyya ita ce farkon kalandar shekara ta Hijira kuma ya sanya kalanda sunanta. Ana amfani da kalandar Hijiriyya don nuna wasu muhimman abubuwan da suka faru na Musulunci da kuma ranaku kamar Ramadan, Eid al-Fitr, Idin Al-Adha da farkon lokacin Hajji.
Mutane suna tambayata
Me yasa shekara ta 622 ta zama shekarar farko a kalandar Musulunci?
Shekara ta farko ta kalandar Musulunci ta fara ne a shekara ta 622 Miladiyya lokacin da Annabi Muhammad SAW da mabiyansa suka yi hijira daga Makka zuwa Madina . Wannan hijirar ita ake ce ma ta “Hijira”. Sannan ana Rubuta shekarar Musuluncin AH, ma’ana “bayan Hijira”
ASALI.
Asalin faruwar Kalandar Hijrar Musulunci, abu ne mai fadi da dogon tarihi, amma dai ta samu asalinta ne lokacin Khalifancin Sayyadina Umar Bin Khaddab (RA.) a sakamakon wani abu mai muhimmanci daya faru a cikin watan Sha'aban wanda Sahabbai suka yi kokarin tantance wane Sha'aban ne amma abin ya faskara. Wannan dalili ne yasa Sayyadina Umar (RA) ya tara Sahabbai inda ya nemi shawarar yadda za'a rika tantance tarihin faruwar al'amura a Musulunci.
Don haka shawara ta tsaya akan fara lissafin kalandar Musulunci daga lokacin da Manzon Allah (S.A.W.) yayi hijra daga Makkah zuwa Madinah, kuma aka sanya watan Muharram ya zama shine watan farko a cikin jerin watannin kalandar Musulunci (Hijrah).
WATANNIN HIJRAR MUSULUNCI
Shekarar Musulunci (Hijrah) tana da watanni goma sha biyu 12 wadannan watanni sune:-
(1) Muharram
(2) Safar
(3) Rabi'ul Awwal
(4) Rabi'ul Thani
(5) Jumada Ula
(6) Jumada Thani
(7) Rajab
(8) Sha'aban
(9) Ramadan
(10) Shawwal
(11) Zhul Qi'idah
(12) Zhul Hajj
WATANNI HUDU MASU ALFARMA
A cikin watanni Hijrar Musulunci guda 12 Allah Madaukakin Sarki ya kebance guda hudu masu Alfarma, sune:-
Muharram wata na (1)
Rajab wata na (7)
Zhul Qi'idah wata na (11)
Zhul Hajj wata na (12)
@Saliadeen sicey
Comments
Post a Comment